INEC za ta gana da Jam'iyyun Najeriya

Shugaban hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben Najeriya za ta gana da jam'iyyun siyasar kasar

A Najeriya, a ranar Laraba ne ake sa ran hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC za ta yi wata ganawa ta musamman da jam'iyyun siyasar kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da sabon shugaban hukumar zaben zai yi irin wannan zama da jam'iyyun siyasar kasar, kuma zaman na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar ke cike da kokwanto game da yiwuwar gudanar da babban zaben kasar a watan Janairu mai zuwa.

A baya dai hukumar karkashin jagorancin sabon shugabanta Farfesa Attahiru Jega, ta gana da kungiyoyi daban daban

Sakataren jam'iyyar ACN ta kasa a Najeriya, Dr. Usman Bugaje ya shaidawa BBC cewar idan sun je taron zasu nemi jin takamaimai irin shirin da hukumar zaben take yi dangane da babban zaben kasar