Obama Musulmi ne - In ji Amurkawa

Shugaba Obama na Amurka

Adadin Amurkawan da suka yi amannar cewa shugaban Amurka Barack Obama Musulmi ne na dada karuwa, in ji wani sakamakon binciken da aka gudanar a kasar.

Binciken jin ra'ayin jama'ar wanda cibiyar Pew Research ta gudanar ya nuna cewa, kimanin kaso 18 cikin dari na Amurkawa sun yi amannar cewa shugaba Obama Musulmi ne, adadin da ya karu daga kaso 11 cikin dari a makamancin binciken da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2009.

Wannan batu ya fi fitowa fili ne a tsakanin 'yan jam'iyyar Republican, inda kashi 34 cikin dari suka ce shugaban kasar Musulmi ne.

An dai gudanar da wannan binciken jin ra'ayin jama'ar ne kafin ran 13 ga watan Agusta lokacin da shugaba Obama ya kare hakkin da Musulmi suke da shi na gina wata cibiyar Musulunci a kusa da inda aka kai harin ta'addanci na ranar 13 ga watan Satumba.

Kaso 43 cikin dari na wadanda aka yi wa tambayoyi dai sun ce ba su san addinin da shugaban kasar ta Amurka ke bi ba.

Sai dai fadar White House ta alakanta abinda ta kira kuskure a kan addinin Mr Obama, ga farfagandar abokan adawarsa.

Fadar ta White House dai ta ce shugaba Obama na bin addininsa na Kiristanci sau da kafa.