Ambaliyar ruwan Pakistan, annoba ce ga duniya - In ji Ban Ki Moon

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Pakistan Shah Mehmood Qureshi, yayi gargadin cewa halin da siyasar kasar ke ciki ka iya fin karfin mahukuntan kasar matukar kasashen duniya suka gaza wajen bada taimako game da bala'in da ambaliyar ruwa ta haifar a kasar.

Shah Mehmood Qureshi ya shaidawa BBC cewa dan abin da ke hannu kasar ta Pakistan ba zai wadatar ba, kuma akwai matukar bukatar a hana masu tada kayar baya su cike gibin da matsalar zata haifar.

Da yake maida martani dangane da zargin da ake yi na cewar gwamnatin Pakistan na jan kafa wajen taimakawa wadanda bala'in ya shafa Mr. Qureshi ya ce, sojojin Pakistan na nan, hukumar bada agajin gaggawa ita ma tana nan, kana kuma gwamnatocin larduna suna hada kai da gwamnatin tarayya don shawo kan matsalar.

Barna mai yawa

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce kimanin mutane miliyan hudu ne dake lardunan Punjab da Singh na kasar Pakistan suka rasa muhallansu sakamakon bala'in ambaliyar ruwan data afku a kudancin kasar.

Kawo yanzu kimanin mutane miliyan takwas ne a fadin kasar ke matukar bukatar taimakon gaggawa, inda kuma a yau ne Majalisar Dinkin Duniya ki shirin gudunar da wani zama na musamman don tattauna matsalar.

Tun da farko dai bankin raya 'kasashen Asiya yayi tayin baiwa kasar Pakistan bashin dala miliyan dubu biyu don taimakawa 'kasar shawo kan matsalolin da ambaliyar ruwan ta haddasa.