Ma'aikatan kwadagon sun shiga yajin aiki a Afirka ta Kudu

Shugaban Afirka ta Kudu Mr. Jacob Zuma
Image caption Ma'aikatan kwadagon Afirka ta Kudu zasu shiga yajin aikin sai baba ta gani

A Afirka ta Kudu, kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki na sai abinda hali yayi, a kan batun albashi.

Ma'aikatan gwamnati fiye da miliyan daya ne ake jin za su tsunduma yajin aikin, inda suke neman a yi masu karin albashin da zai ninka hauhawar farashin kaya.

Tuni dai wasu rahotanni ke cewa an tilastawa wasu makarantu da wani asibiti, rufe kofofinsu

Su dai kungiyoyin kwadagon na bukatar karin kimanin kaso tara ne cikin dari.

Wani jagoran 'yan kwadagon, Thobile Ntole ya ce yajin aikin zai shafi daukacin ma'aikatun gwamnati.

A makon jiya ne dai ma'aikatan suka yi jerin gwano na yini guda inda suka mika bukatunsu ga jami'an gwamnati a garuruwan Pretoria da Cape Town.