Mutane da dama sun mutu a Aljeriya

Sojojin Aljeriya
Image caption Jami'an tsaron kasar Aljeriya

Jami'an gwamnatin Aljeriya sun ce mutane da dama ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a kasar.

Jami'an tsaro na sa kai sun ce mutane uku sun mutu a garin Djelfa, yayin da santsi ya kwashe motar da suke ciki.

An kuma bayar da rahoton rufe manyan tituna da dama a kasar ta Aljeriya.

Ambaliyar ruwan dai ta faro ne tun daga ranar Laraba, bayan an kwashe tsawon lokaci ba tare da an samu ruwan sama ba.