Malalar mai a yankin Niger Delta

Malalar mai a yankin Niger Delta na ci gaba da gurbata muhalli
Image caption Malalar mai a yankin Niger Delta na ci gaba da gurbata muhalli.

Malalar danyen man fetur na daya daga cikin matsalolin da ke cima al'umomin yankin Naija Delta dake Kudu Maso Kudancin Najeriya, tuwo a kwarya. Malalar man dai na faruwa be sanadiyar fashewar bututun man da kamfanonin hakar manfetur suka shimfida a sako sakon yankin. Fashewar bututun na Kwana Kwana nan dai, ya faru ne a gari Bonny dake Jihar ribas Ribas, daya daga cikin cikin jihohin yankin, a inda bututun man Kamfanin Shell ya fashe , wanda kuma ya yi sanadiyar gurbata ruwan da al'ummar wurin suka dogara da shi wajen Sana'ar kamun kifi da wasu al'amuran yau da kullum. Wani dattijo a kauyen wanda ya ki a bayana sunansa ya shaidawa BBC cewar; " Mun fara lurane da malalan man tun ranar uku ga watan Agusta, kuma muka sanar da hukumar awa shegarin ranar, amma har yanzu ba a kawo mana wani dauki ba".

A yayin da yake wa BBC bayani, daya daga cikin dattijan wannan Kauye, wanda bai baiyana sunan sa ba,"yace mun fara lurane da malalan man ne tun ran Uku ga watan Agusta, kuma muka sanar wa hukuma a ranar Hudu ga watan,amma kuma har har yanzu ba a kawo mana wani dauki ba."

Wani mai sana'r kamun kifi a garin Bonny, mai suna , Mr Sonny Wilkosta ya shaidawa BBC cewar gurbacewar ruwa ta lallata musu ragar kamun kifi da kuma wasu daga cikin kayayayyakin da suke amfani da su wajen sana'ar su. Ko da yake, a sakon da Kamfanin na Shell ya aikewa manema Labarai, Kamfanin ya ce , Malalan man na faruwa ne sakamakon fasa bututun mai da suke zargin barayin danyen mai suka yi ne , a daya daga cikin bututun na Shell da ke Shimfide a gefen Kogin garin Bonny. Ana dai ganin cewa, batun malalan mai daya zama ruwan dare, a yankin Naija Delta, na faruwa ne a dalilin rubewan Bututun mai , ko kuma fasa bututun da Barayin mai ke yi.