An yi kira da a kara tallafawa Pakistan

Ambaliyar Pakistan
Image caption Jama'a na rububin karbar taimakon shinkafa daga sojojin kasar ta Pakistan

An yi kira da babbar murya ga kasashen duniya su kara kaimi wajen samar da agaji ga kasar Pakistan, sakamakon bala'in ambaliyar ruwan da kasar ke fuskanta.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, da kuma Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, da ma ministan hulda da kasashen wajen Pakistan ne suka yi wannan kiran a wurin taron da Majalisar ta kira.

Kashi daya bisa biyar na fadin kasar ne dai ruwa ya mamaye, yayin da mutane miliyan 20 ke bukatar abinci da muhalli.

Mr Ban ki Moon, wanda bai dade da dawowa daga kasar ta Pakistan ba, ya siffanta abinda ya gani a can, inda ambaliya ta yi awangaba da garuruwa da dama, sannan ta jefa rayuwar jama'a cikin mawuyacin hali.

Ya ce kasar na bukatar daukin kasashen duniya domin shawo kan abin da ya bayyana da cewa, kalubale ne da ke fuskantar duniya ba ki daya.

'bala'in da yayi kama da tsunami'

Mista Moon ya ce bannar da ambaliyar ta haifar itace mafi girma idan aka kwatanta da makamantanta hudu da aka yi a baya-bayannan, wato girgizar kasar Haiti data Kashmir da kuma bala'in Tsunami.

Har ila yau ya yi gargadin cewa tasirin bala'in ka iya daukar tsawon lokaci.

Yace: "Pakistan na fuskantar bala'in da yayi kama da tsunami, wacce girmanta ka iya karuwa nan da wani dan lokaci".

Ana danganta jan kafar da kasashen duniya ke yi wajen taimakawa da karancin karuwar wadanda suka mutu a bala'in, sai dai wasu na ganin kaurin sunan da kasar ta yi wajen cin hanci da rashawa na yin tasiri.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta ce jama'ar Pakistan na bukatar su tabbatar da cewa shugabannin su basu karkatar da kudaden agajin da aka samarba.