SPLM ba za ta halarci taron Sudan ba

Taswirar Kudancin Sudan
Image caption Ana shirye-shiryen gudanar da zaben raba-gardama a kan ko yankin Kudancin Sudan zai balle daga kasar

Tsohuwar kungiyar 'yan tawayen kasar Sudan, wato SPLM, ta ce ba za ta halarci taron da shugaban kasar, Omar el-Bashir, ya kira yau ba dangane da zaben raba gardama a kan samun 'yancin kudancin kasar.

Ita dai SPLM ta ce ba a tuntube ta ba yayin da ake shirya taron na yau.

Sai dai babban sakataren kungiyar, Pagan Amum, ya shaidawa BBC cewa kungiyar tasu za ta ci gaba da tattaunwa da jam’iyyar Shugaba el-Bashir din a kan zaben raba-gardamar.

Ko a watan da ya gabata ma an soke yin irin wannan taro bayan kungiyar ta SPLM da ma wasu jam'iyyun adawar da dama sun bukaci a tattauna batutuwan da suka hada da rikicin yankin Darfur a wurin taron.