Majalisar Dinkin Duniya za ta tattauna kan Pakistan

Ban Ki Moon a Pakistan
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya kai ziyara ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya za ta yi wani taro na musamman don tattaunawa a kan bala'in ambaliyar ruwan da ta shafi kasar Pakistan.

Ana kuma sa ran Babban Sakataren Majalisar, Ban Ki Moon, zai yi jawabi ga babban zauren Majalisar a kan abin da ya ganewa idanunsa a ziyarar da ya kai kasar ta Pakistan, da yin kira ga kasashen duniya su kara kaimi wajen ba da taimakon gaggawa kamar yadda Majalisar ta nema.

Mista Ban dai, wanda ya sha ganin ta'adin da bala'o'i kan haifar, ya bayyana cewa bai taba ganin wani bala'i irin wannan ba yayin ziyarar tasa zuwa Pakistan.

A cewarsa, ambaliyar ruwan ta yi kaca-kaca da kashi daya cikin biyar na daukacin kasar Pakistan, inda ta yi awon gaba da garuruwa da kauyuka ta kuma jefa miliyoyin mutane cikin halin ni-'ya-su.

Majalisar Dinkin Duniyar ta fara nuna kyakkaywan fatan samun agaji bayan rashin tabbas na dan wani lokaci.

Ya zuwa yanzu dai al'ummar duniya ta alkawarta samar da fiye da rabin kudaden da Majalisar ta nema na taimakon gaggawa.

Mutanen Pakistan sun bayyana takaicinsu da yadda kasashen duniya suka yi shakulatin bangaro da bukatar agajin.

Sai dai taron na Majalisar Dinkin Duniya ba na tara gudummawa ba ne, kuma ba a sa ran zai samar da wani kwakkwaran shiri na ba da tallafi.

Kasancewar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, za ta yi jawabi a wajen taron, ya nuna cewa taron wani yunkuri ne na zaburar da duniya dangane da wannan bala'i wanda zai dauki lokaci yana tasiri a kan kasar ta Pakistan, wacce kasa ce mai muhimmanci a yakin da ake yi da Taliban da kuma Alka'ida.

Babbar bukatar dai ita ce a ceto rayukan wadanda abin ya shafa, to amma taron zai bukaci kasashen duniya su tallafawa yunkurin magance wahalhalun da ambaliyar za ta haifar na tsawon lokaci.

Karin bayani