Rundunar Amurka ta karshe ta bar Iraki

Sojojin Amurka a Iraki
Image caption Runduna ta karshe ta Amurka ta fice daga Iraki kafin cikar wa'adinta

Rundunar Amurka ta karshe da ke fagen daga a Iraki ta bar kasar makwanni biyu kafin lokacin da aka tsara ficewarta.

Ficewar rundunar dai, bayan ta shafe shekaru bakwai da rabi a Irakin, wani muhimmin mataki ne, kuma gwamnatin Obama ta bayyana cewa za a janye wasu dakarun dubu biyar zuwa dubu shida daga bakin daga a karshen wannan watan.

Tun bara ne dai aka fara rage dakarun Amurka da ke kasar ta Iraki.

To amma da janye wannan runduna ta hudu ta mayakan da ke dauke da manyan makamai, a iya cewa aikin ya zo karshe.

Dakaru dubu hamsin za su ci gaba da kasancewa a Irakin don tallafawa gwamnatin kasar a yunkurin ta na tabbatar da doka da oda.

Kuma ko da yake za su rike makamai, wadannan dakarun za su yi amfani da makaman ne kawai don kare kai; ba kuma za a yi sauyi a jadawalinsu ba sai in gwamnatin Irakin ce ta nemi hakan.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, P.J. Crowley, ya ce Amurka ba ta kawo karshen damawar da a ke yi da ita a Iraki ba, sai dai za ta rage yawan katsalandan din da ta ke yi kuma za ta fi mayar da hankali ne ga ayyukan da ba na soji ba.

Ya kuma ce Amurka na da jarin da ya kai na dala triliyon daya da za ta ba kariya a Irakin.

A ranar 31 ga watan Agusta ne dai ake sa ran Shugaba Obama zai bayar da sanarwar kawo karshen yakin 'yantar da Iraki.