Shekara guda bayan sakin al-Megrahi

Komawar al-Megrahi kasar Libya bara
Image caption An saki Abdelbasit Ali al-Megrahi ne a bisa dalilan jinkai

Burtaniya ta shaidawa Libya cewar bai kamata ta ce za ta yi wani bikin cika shekara guda da komawar Abdulbasit El-Megrahi gida ba, mutumin da aka samu da laifin tarwatsa jirgin saman Amurka a sararin samaniyar Lockerbie a 1988.

Gwamnatin Burtaniyar ta ce duk wani biki na nuna farin ciki da sakinsa, ba za a yi marhabin da shi ba, zai kuma bakanta rai, ya kuma nuna cewar ba a damu da halin da wasu suka shiga ba.

An saki El-Megrahi ne daga wani gidan kaso na yankin Scotland, bayan da aka gano cewar yana fama da wata cutar cancer, wadda ba ta tashi ba, amma kuma har yanzu yana nan a raye.

Shekara guda

Shekara guda ke nan cif-cif tun bayan sakin dan kasar Libyan nan da aka samu da hannu a tarwatsa jirgin saman Amurka a garin Lockerbie.

Mutane dari biyu da saba'in ne kuma suka rasa rayukansu lokacin da jirgin saman na Pan Am ya tarwatse a kudu maso yammacin yankin Scotland.

Abdelbasit Ali al-Megrahi ne kadai dai aka hukunta a bisa laifin aikata wannan ta’asar a shekarar 1988.

Ga duk mutum guda da ya rasa ransa kuma, dan kasar Libyan ya yi zaman gidan kaso na makwanni biyu, kafin Sakataren Shari'a na yankin Scotland, Kenny MacAskill, ya ba da sanarwar sakinsa a bisa dalilan jinkai.

Al-Megrahi dai na fama da ciwon sankara, to amma an samu sauyi a bisa shawarar likitocin da ta ba shi damar samun 'yanci.

Daraktan lafiya na gidan kason da aka tsare shi, Andrew Fraser, ya ce zai rasu ne cikin watanni uku, amma kawo yanzu ya rayu ninkin haka har sau hudu.

Babban ministan yankin Scotland, Alex Solomon, zai kare matakin sakin al-Megrahi nan gaba a yau, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun korafi daga Amurka, inda 'yan Majalisar Dattawa suka fara wani bincike kan ko sakin nasa na da alaka da yarjejeniyar man fetur tsakanin kasar Libya da kamfanin mai na BP.

Gwamnatin Scotland dai ta nace cewa ba alakar tattlin arziki, ko siyasa ko ma diflomisiyya ne suka sa aka saki mutumin da ya haddasa harin ta'addanci mafi muni a tarihin Birtaniya ba.

Matsin lambar kasuwanci

Wasu 'yan majalisar dattawan Amurka hudu sun sake kiran da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan sakin nasa.

Yan majalisar dattawan biyu na Amurka sun fitar da abinda suka ce sheda ce ta matsin lambar kasuwanci don sakin Abdelbaset Ali Al-Megrahi, shekara daya cif cif da ta wuce.