'Dokar zabe ta je fadar gwamnati a makare'

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Bangaren zartarwa na gwamnatin Najeriya ya ce dokar da 'yan Majalisar Dokoki suka yiwa gyara ba ta isa gaban Shugaba Goodluck Jonathan ba sai farkon makon nan

A Najeriya, yayin da ake tsammanin cewa sabuwar dokar zabe da kwarya-kwaryar kasafin kudin da majalisun dokokin kasar suka zartar sun dade da isa gaban shugaban kasar domin ya sa hannu, rahotanni na nuna cewa bai yi tozali da su ba sai a farkon makon nan.

Mai ba shugaban kasar shawara a kan ayyukan majalisa, Sanata Abba Aji, ya shaidawa BBC cewa; "Dokokin zabe, da kasafin kudin Hukumar Zabe gaba daya, sun iso wurinmu ranar Litinin da dare, kuma a daren aka kai, to [Shugaban Kasa] ba zai samu ganin takardun nan ba sai ranar Talata".

Bayanai dai sun nuna cewa an samu jinkirin ne a wani sashe na Majalisar Dokoki ta Kasa, wanda ke da alhakin daidaita dokokin kafin a aikewa shugaban kasar.

A cewar Sanata Abba Aji, 'yan majalisar sun gama da wadannan dokoki, "to amma a Majalisar, akwai wani [sashe da ake kira] Legal Department, wato [sashen da ke kula da] sha'anin shari'a.

"Su ne za su duba su tabbatar da cewa ya dauki fasalin doka, sannan zai iso wajenmu".

Sanata Abba Aji ya kuma ce 'yan majalisar suna da gaskiya idan suka ce sun gama aiki a kan dokokin, kuma yana sa ran Shugaba Goodluck Jonathan zai sa hannun a kan dokokin kafin karewar makon nan.

'Yan majalisar dai sun ce tun bayan zartar da dokokin suka mika su ga bangaren zartarwar.

Jinkirin sanya hannun shugaban kasar dai na ci gaba da janyo cece-ku-ce a Najeriya.