Isra'ila da Falatsdinawa sun nuna fata nagari

Shugaban Isra'ila da na Falatsinawa
Image caption Duka bangarorin biyu sun nuna fata na gari, amma jama'ar kasar na nuna shakku

Shugabannin Falasdinawa da na Isra'ila sun yi maraba da tayin da Amurka ta yi musu na komawa tattaunawa kai tsaye a watan gobe.

Bangarorin biyu dai sun bayyana cewa a shirye suke su koma kan teburin shawarwarin a Washington ranar biyu ga watan Satumba.

Sai dai wakilin BBC Wyre Davies, dake birnin Kudus, ya ce mutanen yankin da dama na nuna shakku a kan yiwuwar samun nasara a tattaunawar.

Babu dai kwakkwarar amintaka tsakanin shugabannin Isra'ila da Falatsdinawa. Amma a 'yan watannin da suka gabata masu shiga tsakani na Amurka sun matsawa bangarorin biyu domin fuskantar hakan.

Fata na gari

Da yake maida martani kan tattaunawar da ake shirin farawa, mai magana da yawun gwamnatin Isara'ila Mark Regev, yace sun dade suna kira da a fara ganawa kai tsaye, kuma ashirye suke domin yin cikakkiyar tattaunawa da Palatsinawa. Shi ma anasa bangaren, babban mai shiga tsakani na Falatsdinawa Saeb Erekat, cewa yayi ya kamata tattaunawar ta zamo mai amfani, sannan yayi fatan bangarorin biyu su tunkari yunkurin samar da zaman lafiyar tukuru.

Sai dai duka a Isra'ila da Falatsdinu, ana nuna shakku kan nasarar da wannan tattaunawar za ta haifar, bayanda aka shafe shekaru 20 ana gudanar da makamanciyarta ba tare da wata nasara ba.

Masu lura da al'amura na ganin akwai matsaloli da dama da ya kamata a shawo kansu, idan har anaso akai ga gaci.