Hukumar IMF za ta gana da Jami'an Pakistan

Dominique Strauss Kahn, Shugaban IMF
Image caption Dominique Strauss Kahn, Shugaban IMF

Asusun bada lamuni na duniya, IMF ya ce ambaliyar ruwan da ta afka ma Pakistan zata kasance wani babban kalubale ta fuskar tattalin arziki ga gwamnatin kasar da kuma al'umarta.

Hukumar ta IMF za ta fara shawarwari da jami'an gwamnatin Pakistan din jibi, Litinin a Washington, inda zasu su yi nazarin irin matakan da Pakistan din ta dauka na tunkarar bala'in, domin sanin irin taimakon da ya fi dacewa su ba ta

Wakilin BC ya ce tuni dai irin tasirin da wannan bala'i ya haddasa ta fuskar tattalin arzikin kasa ya fara bayyana, wajen tashin farashin wasu kayayyakin abinci, sakamakon lalacewar hanyoyin rarraba su.

Taron zai kuma sake nazari kan yadda ambaliyar ruwan zata shafi bashin da yanzu haka kungiyar IMF din ke bin Pakistan din na dala biliyan goma.

Pakistan dai ta yi kiyasin cewar ambaliyar ruwan za ta haddasa gibin kasafin kudin da aka kiyasta zai ribanya ya zuwa fiye da kashi 8 cikin dari.