Hukumar lamuni ta IMF za ta gana da Jami'an Pakistan

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta ce za ta fara tattaunawa da jami'an gwamnatin Pakistan jibi, Litinin a Washington, domin kimanta girman asarar da kasar ta tafka ta fuskar tattalin arzikin kasa, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye kashi daya cikin biyar na kasar.

Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mahmoud,ya ce yana jin da farko al'ummar duniya ba ta fahimci girman bala'in da kasar ke fuskanta ba, sai da kafafe irinsu BBC suka taimaka .

Wani babban jami'in hukumar ta IMF ya ce zasu yi nazarin irin matakan da Pakistan din ta dauka na tunkarar bala'in, domin sanin irin taimakon da ya fi dacewa su ba ta.

Pakistan dai ta yi kiyasin cewar ambaliyar ruwan za ta haddasa gibin kasafin kudin da aka kiyasta zai ribanya ya zuwa fiye da kashi 8 cikin dari.