Kotu ta haramta wa wasu ma'aikata yajin aiki a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi nasarar samun wani hukuncin kotu da ya haramtawa ma'aikatan da ayyukansu ke da matukar muhimmanci ci gaba da yajin aiki na kasa baki daya.

Hukuncin ya kuma haramtawa nas nas da malaman makaranta daga razana abokan aikinsu da suka ki shiga yajin aikin, wanda yau kwana hudu da farawa.

Wani kakakin kungiyoyin kwadago, Mugwena Maluleke ya ce, ba za su mu shawarci yan kungiyar da su koma bakin aiki ba, saboda wadanda suka dauke su aiki, ba su damu da bukatunsu ba. Ya ce, sun ki su share ma su hawaye.

Ministan kiwon lafiya na Afrika ta Kudu ya zargi masu yajin aikin da jefa rayukan marasa lafiya cikin hadari, ta hanyar rufe kofofin shiga asibitoci