An samu ci gaba a neman maganin cutar Ebola

Wasu masana kimiyyar Amurka sun ce sun samu muhimmin ci gaba wajen hada wani maganin cutar nan mai kisa ta Ebola.

Cutar ta Eboladai ta kashe mutane sama da dubu daya a Afrika, cikin shekaru talatin da suka wuce.

Ana kuma nuna fargabar cewa 'yan ta'adda na iya amfani da kwayar cutar wajen kai hare hare.

A lokacin da suke wallafa sakamakon binciken na su, a mujallar likitoci ta Nature Medicine, sun ce sabon maganin yayi aiki cikin sa'a guda da baiwa wasu birai da suke dauke da cutar ta Ebola, da kamar kashi sittin cikin dari.

A yanzu hukumomin lafiya na Amurka sun bada izinin a yi gwajin maganin kan bil'adama, amma jami'an kiwon lafiya na gargadin cewa za a dauki lokaci kafin bada lasisin aiki da maganin.