Jama'iyar PDP ta lashe zaben cike gurbi a Gombe da Bauchi

A Najeriya an fitar da dukanin sakamakon zaben cike gurbin da aka yi jiya a jihar Gombe.

An yi zaben ne dai samakon mutuwar wadanda ke rike da mukaman tun farko.

Jama'iyar PDP ce dai ta lashe dukanin kujerun.

Sai dai masu sa ido kan zaben sun yi zargin cewar zaben ya fuskanci kurarai da suka hada da satar akwatunan zabe da yar hatsaniya.

Wadannan zabuka dai sun kasance zakaran gwajin dafi ga hukumar zabe ta kasar mai shirin gudanar da zaben kasa baki daya na farkon shekara mai zuwa.