Ambaliyar ruwa na ci gaba da barna a Pakistan

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Ambaliyar ruwa a lardin Sindh na kudancin Pakistan ta yi awon gaba da wani shinge da aka yi na laka, domin kare birnin Shahdadkot daga ambaliya.

Wani wakilin BBC da ya kai ziyara yankin ya ce, da ma dai sojoji ne da wasu ma'aikatan agaji suka gina katangar cikin hanazari, kuma ga shi a yanzu ruwa ya kayar da ita, ya kuma tasamma garin, wanda kusan yanzu babu wani mahaluki a cikinsa.

Ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mahmud Qureshi ya yaba da gudunmawar da ake ba su;ya ce,"mun yaba da irin agaji da goyon bayan da ake baiwa Pakistan. Ina mika godiyarmu a madadin daukacin al'umar Pakistan".

Kungiyoyin agaji na ta daukar matakan yaki da cutukan da suka barke masu nasaba da gurbataccen ruwa, musamman a arewacin kasar.

Har yanzu dai al'amura a kasar babu kyaun gani; mutane da dama ba sa samun taimakon da suke bukata, suna kuma fama da rashin muhalli, da karancin abinci, da kuma karancin magunguna, yayin da suke fuskantar yiwuwar barkewar cututtuka.

Gwamnatin kasar ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan wannan bala'in wanda ba a taba ganin irinsa ba, duk kuwa da karancin kudi da kayan aikin da ake bukata don fuskantar matsalar.

Masu suka dai sun zargi gwamnatin da rashin iya aiki da ma nuna halin ko-in-kula wajen fuskantar matsalar.

Wannan dai wata mummunar shaida ce da ka iya bata sunan gwamnatin ta Pakistan wadda da ma ake mata kallon rauni da rashin farin jini.