Ana nuna shakku game da makomar kanen wani janar dan kasar Rwanda dake gudun hijira

Har yanzu dai ba a ji duriyar kanen wani janar dan kasar Rwanda dake gudun hijira ba, bayan da sojoji suka kama shi ranar Juma'a.

Mai dakinsa ta ce tana fargabar kada a halaka shi.

Cikin wata hira da BBC, Peace Rugigana ta ce ta ziyarci gidajen kaso biyu ba ta gan shi ba.

Ta ce, "Sun ce min yana Kigali, na kuma ziyarci gidajen yari biyu, inda ya kamata a ce an tsare shi, amma sun ce ba ya cikin jerin sunayen wadanda suke tsare da shi".

Rundunar sojan Rwanda a jiya ta bayyana cewa, mutumin da aka kama, Laftanar Kanar Rugigana Ngabo, yana da hannu a wani shiri dake barazana ga tsaron kasa.