Jam'iyyar ANPP na shirin zuwa kotu akan zaben Bauchi

Jahar Bauchi a taswirar Najeriya
Image caption Jahar Bauchi a taswirar Najeriya

Jam'iyyar ANPP a jihar Bauchi ta ce tana shirin zuwa kotu, domin kalubalantar zaben Alhaji Adamu Ibrahim Gumba, a matsayin dan majalisar dattawa daga mazabar Bauchi ta Kudu.

A ranar asabar da ta gabata ce aka gudanar da zaben cike gurbi, domin samun wanda zai maye gurbin Sanata Bala Muhammad, wanda aka bai wa mukamin minista.

To sai dai jam'iyyar ANPP a jihar ta Bauchi ta ce an yi magudi a lokacin zaben, don haka tana duba yiwuwar zuwa kotu.