Matsalar ambaliyar ruwa a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya a Pakistan ta bayyana halin da ake ciki na ayyukan jinkai ga wadanda bala'in ambaliyar ruwa ta rutsa da su, da cewa yanayin yayi tsanani.

Yayinda ruwa ke ci gaba da malala kudanci, dubun dubatar mutane na ci gaba da rasa matsugunansu.

Kiyasin da Majalisar Dinikin Duniyar ta yi na nuna cewa a yanzu adadin mutanen da ke bukatar matsuguni cikin gaggawa sun karu daga mutane miliyan biyu zuwa.

A wannan makon ake cika wata guda da fara wannan ambaliyar ruwa, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce duk da ta tara kashi saba'in cikin dari na kudaden da take bukata domin bada agajin gaggawa, har yanzu akwai mutane masu yawa da ba su samu wani agaji ba.