An kawo karshen garkuwa da mota a Philippines

Garkuwa da mota a Philippines
Image caption Garkuwa da mota a Philippines

Wasu 'yan yawon shakatawa 8 daga Hong Kong sun hallaka, lokacin da aka yi garkuwa da motar bas din da su ke ciki a Manila, babban birnin kasar Philippines. Wasu mutanen 7 kuma suna kwance a asibiti.

'Yan sanda sun hallaka mutumen da yayi garkuwa da motar - watau wani tsohon dan sanda wanda bai ji dadin sallamar da aka yi masa daga aiki ba saboda rashin da'a.

Tsohon dan sandan ya kwashe sa'o'i tara yana garkuwa da motar kamin jami'an tsaron su hallaka shi, kuma an rika watsa irin abubuwan da suke faruwa kai tsaye ta gidan talabijin din kasar ta Philippines.

Shugaban Philippines, Benigno Aquino, ya ce ya ji takaicin mutuwar fararen hular da ba ji ba su gani ba.