Kwamitin bincike a kan masarautar Bakura

Jahar Zamfara
Image caption Jahar Zamfara

Hukumomin jihar Zamfara sun kafa wani kwamiti mai mutane tara, domin bincikar zargin karkata akalar wasu kudade, da kuma keta dokar aiki da ake yiwa sarkin masarautar Bakura, Alhaji Bello Sani.

A makon jiya ne gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar dakatar da basaraken, wanda dan uwan tsohon gwamnan jahar ne, Alhaji Ahmed Sani, Yariman Bakura.

Magoya bayan Sarkin dai sun kira dakatarwar da kuma kafa kwamitin a matsayin bita da kullin siyasa.