Kabilar Igbo na son ci gaba da tsarin karba-karba

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, al'ummar Ibo da ke shiyyar kudu maso gabashin kasar sun bukaci a ci gaba da amfani da tsarin na karba-karbar mulki.

Hakan na zuwa yayin da batun ke ci gaba da mamaye muhawarar da ake yi game da al'muran siyasa da kuma zaben shekara ta dubu biyu da sha daya.

Sai dai kuma sun fi so a rika aiwatar da shi shiyya-shiyya maimakon tsakanin bangaren kudu da na arewa.

Sannu a hankali, batun neman a ci gaba da yin amfani da tsarin karba-karbar mulki, yana ta samun karin tagomashi a tsakanin mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya da dama.

Tsarin shiya shiya

Ko da yake masu wannan ra'ayi sun fi so ne a rika gudanar da shi daki da daki a tsakanin shiyyoyin kasar. Ambasada Ralph Uwechue, shugaban kungiyar kare muradun al'ummar Ibo ta Ohaneze na kasa, yana daga cikin masu ganin dacewar bin wannan tsari: "Najeriya tana da shiyyoyi shida, al'ummar Ibo sun yi amanna da haka. Mun kuma yi amanna cewa, kamata ya yi a tafiyar da komai bisa tsari na adala a tsakanin dukkan wadannan shiyyoyi".

Mista Ralph ya kara da cewa; "Mu a wajenmu, ba wai batu ne na karba-karba a tsakanin bangaren arewaci da kudancin Najeriya ba, magana ce ta zagayawa da tsarin tiryan-tiryan a tsakanin shiyyoyin shida da ake da su. Kuma wannan ita ce fassarar tsarin karba-karba a wajenmu."

Masu wannan ra'ayi dai suna ganin ta haka ne kawai kwarya mulkin Najeriya za ta kai ga shiyyoyin da aka yi wa yada kanen wani, inji Ambasada Ralph Uwechue: "Muddin dai ana zancen shugabancin kasar nan ne, shiyyoyin kudu maso kudu da kudu maso gabas ne kadai ba su dana wannan kujera ba. Saboda haka, muke neman su ma a ba su dama ta hanyar karba-karbar. Idan aka yi haka, sai tsarin ya ci gaba da gudana babu wata gargada." Galibi dai, masu cece-kuce kan tsarin na karba-karbar mulki dai, sukan mayar da hankali ne ga manyan bangarori biyu na Najeriya, wato kudanci da arewacin kasar. Abin da a yanzu wasu ke ganin da sake.