Lauyoyi na son samun nagartacciyar gwamnati

Tawirar Najeriya
Image caption Tawirar Najeriya

Lauyoyi a Najeriya sun nuna bukatar da ake da ita ta samun gwamnati ta gari domin tabbatar da cigaban kasar.

Lauyoyin, da ke gudanar da wani babban taro a Kaduna, na tattaunawa ne bisa al'amuran da suka shafi siyasa da zamantakewa a Najeriya shekaru 50 bayan samun yancin kai a kasar.

Lauyoyi sama da dubu goma ne dai ke halartar wannan taro wanda za'a shafe mako guda ana gudanarwa.