Ambaliyar ruwa ta dada dagula al'amura a Nijar

Ambaliyar ruwa a Nijar ta lalata kayan abinci
Image caption Ambaliyar ruwa a Nijar ta lalata kayan abinci

Kungiyar bada agaji ta Oxfam tace kasar nijar na fama da abinda ta kira masifu guda biyu.

Kungiyar ta ce ambaliyar ruwan baya-bayan nan ta dada dagula yanayin rashi abincin da kasar take cikin.

Ma'aikatan agajin da dama na kokarin taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasar.

Oxfam ta ce yanayin ambaliyar ya karar da duk wadansu kayayyakin abinci da kasar ke da su.

Kimanin mutane miliyan takwas ne,wato kusan rabin mutane kasar ke fama da yunwa sakamakon fari.

Kazalika,a yanzu kimanin mutane dubu dari sun bar gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan wace ta mamaye gidajen nasu..

Kungiyar Oxfam ambaliyar ruwan na tarnaki ga aikin kai agaji zuwa kasar.

Ta yi kira ga masu tallafi na kasashen duniya su tallafawa kasar