Saudi Arabiya ta yi karin haske kan matakin aikin Hajji

A Najeriya,jakadan kasar Saudi Arabiya ya yi karin haske kan batun hana wasu 'yan Najeriya zuwa aikin hajji,inda ya ce kasarsa ta yi hakan ne don saukaka aikin Hajji ga maniyata.

Khalid Abdu rabbuhu ya ce wannan doka ta shafi dukkan kasashen duniya ne, don haka baiga dalilin da zaisa Najeriya ta tayar da jijiyar wuya ba.

Sai dai a martanin data mayar,hukumar kula da aikin haji ta kasa ta ce za ta nemi kasar Saudiyya ta sauya dokar nan da ta sa ta hana maniyatan da suka taba zuwa aikin hajji shekaru biyar da suka wuce bisa yin aikin hajji daga bana.

Hukumar dai ta ce ta riga ta kammala shirye shiryen aikin hajjin bana, kuma dokar da kasar Saudiyya ta fitar ta fito ne a kurarren lokaci ganin irin tanadin da hukumar ta yi wa maniyyatan.

Ofishin jakadancin Saudiyya dake Najeriya ya shaidawa hukumomin kasar cewa, daga bana maniyyata za su iya yin aikin hajji ne sau daya cikin shekaru biyar.