Ana ci gaba da kwashe 'yan Pakistan daga wajen ambaliyar ruwa

Wasu mutane da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan
Image caption Ana ci gaba da kwashe wadanda ambaliyar ruwan ta shafa

Jami'an agaji a Pakistan sun kwashe tsawon daren jiya alhamis suna korakin kwashe kimanin mutane dubu dari biyar daga kauyukan dake yankin Sindh dake Pakistan.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya kuma na yin barazanar sake sabunta wata ambaliyar ruwa a kauyukan dake lardin.

Jami'in majalisar dinkin duniya,Mista Holmes ya ce bada tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su na bukatar jiragen helicopter guda arba'in cikin gaggawa

Ya ce ta sama ne kawai tallafin zai iya isa ga kimanin mutanen Pakistan dubu dari takwas.

A halin da ake ciki abinda ke kare ambaliyar daga shafarsu shi ne wani dam da ya raba yankin da sauran yankuna.

Sai dai shima dam din ya nuna alamar ballewa.

Ambaliayar ruwan a lardin na Sindh na dada kawo fargaba wajen kai agajin gaggawa.

Kuma gwamnati ta ce kusana mutane miliyan ashirin ne ambaliyar ruwan ta shafa,kuma kimanin miliyan biyar basu da wajen kwana.