Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugaban kasa

A Nijeriyar wasu mukarraban shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan sun tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba ne shugaban zai bayyana wa duniya aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben badi.

A cewarsu shugaban kasar zai jinkirta bayyana aniyar tasa ne a karshen watan azumi domin a samu damar yin kasaitaccen biki.

Wannan dai zai kawo karshen tababar da ake yi game da tsayawa takarar shugaban kasar.

Sai dai kuma a daya hannun yunkurin shugaban kasar ka iya fuskantar kalubale daga wasu dattawan arewacin kasar wadanda suka ce lallai sai mulki ya koma arewa badi.