Shugaba Jonathan zai tsaya takara

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriyar wasu mukarraban shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan sun tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba shugaban kasar zai bayyana wa duniya aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben badi.

A cewarsu shugaban kasar zai jinkirta bayyana aniyar tasa ne zuwa karshen watan azumi domin a samu damar yin kasaitaccen biki. Wannan dai zai kawo karshen tababar da ake yi game da tsayawa takarar shugaban kasar.

Sai dai kuma a daya hannun yunkurin shugaban kasar ka iya fuskantar kalubale daga wasu dattawan arewacin kasar wadanda suka ce lallai sai mulki ya koma arewa badi.

Bayan an kwashe zamani mai tsawo ana jujjuya batun tsayawar shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan takarar shugabancin kasar a babban zaben badi cikin wani yanayi mai daurewar kai, yanzu dai na hannun daman shugaban sun ce maganar tsayawarsa takara ba wai a ciki.

Zai tsaya bayan azumi

Sanata Abba Aji mai baiwa shugaban kasar shawara a kan ayyukan majalisun dokokin kasar ya ce; " Shugaba Jonatha zai bayyanawa 'yan Najeriya bukatarshi na tsayawa takaran shugabanci kasar a shekarar 2011, amma sai bayan azumi zao bayan hakan saboda shima yana azumi kuma zai tsaya ne a jamiyyar PDP".

"Baya fargabar tsayawa da kowa. Da janar Babangida da Atiku, tun da sun taba shugabanci kasar nan kuma su manya ne, ina ganin za su janye su bari Jonathan ya tsaya takara." In ji Sanata Abba Aji.

Sai wasu dattawa `yan bangaren arewacin Najeriyar da ke wata kungiya mai suna Northern Elders Assembly, masu ra`ayin lallai sai jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ta bi tsarin karba-karba wajen bai wa dan arewa damar tsayawa takara a badi sun ce ba za su goyi bayan tsayawa takarar Dr Goodluck Jonathan din ba.

Akwai kalubale a gaba

Har ma suka yi wa jam`iyyar PDPn hannunka-mai-sanda, Mallam Adamu Chiroma wani mamba a kungiyar ya ce; "Babu kungiya kamar jamiyyar siyasa wanda bazata raunana ba idan bata yin adalci da gaskiya. Idan an tsaida Jonathan a PDP, za'a fuskanci wasu 'yan takara daga wasu jam'iyyu kuma masu zabe za su zabi wadanda suka ka ya dace."

Sai dai Senata Abba Aji ya ce da yawun jam`iyyar PDP Dr Goodluck Jonathan din zai tsaya takara don haka ba matsala.

Image caption Tsohon mataimakin Shugaba kasa a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar shima ya bayyana aniyarsa na takarar shugabancin kasar.

"Ko kadan bazamu samu matsala ba. Da gwamnonin PDP gabaki daya da kuma shugabannin jam'iyyar mun halara a wani taro, kuma duk sun amince da tsayawar Shugaba Jonathan".

Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasar dai watakila zai faranta wa wasu jam`iyyun adawar kasar wadanda ke lissafin cewa hakan ka iya jefa jam`iyyar PDPn cikin rudani su kuma su ci bulus, amma jam`iyyar pdp a nata banagaren ta ce ta saba da daidaita al`amura a duk lokacin da gidanta ya dauki-dumi.