Barazanar barkewar cutar Kwalara a Najeriya

Akalla sama da mutane 300 sun mutu sanadiyar cutar kwalara a Najeriya
Image caption Akalla sama da mutane 300 sun mutu sanadiyar cutar kwalara a Najeriya

Hukomomin kula da lafiya a Najeriya sun ce akwai barazanar barkewar cutar kwalara a kasar baki daya.

Akalla mutane 352 ne suka mutu a sanadiyar cutar a cikin watanni uku. Haka kuma wasu mutane sama da dubu shida suna jinya a arewacin kasar sakamakon kamuwa da cutar.

Likitoci a jihohi goma sha biyu a kasar suna sa'ido kan yaduwar cutar.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta alakanta barkewar cutar da yanayin damina da ake ciki, yayinda wasu ke ganin ambaliyar ruwa ce ta gurbata ruwan sha a yankunan karkara a kasar.

Toshe magudanar ruwa

Sannan kuma a wurare da dama akwai karancin dakunan ba haya, sannan kwatoci na saurin cika da shara dake hana ruwa gudu kamar yadda ya kamata.

A wata sanarwa da Ma'aikatar ta fitar ta ce; "Bincike ya nuna cewa, akwai barazanar cewa za'a samu barkewar cutar a kasar baki daya."

A kasar Kamaru ma dai barkewar cutar kwalarar ta kashe sama da mutane dari biyu.

Image caption Ana dai kamuwa da cutar kwalara ne ta gurbataccen ruwa

Ana dai kamuwa da cutar kwalara ne ta gurbataccen ruwa, kuma cutar na haddasa amai da gudawa, wanda idan ba'a magance shi da wuri ba na iya kaiwa ga kisa.

Ba wuya akan kamu da cutar, kuma za a iya kaucewa kamuwa da cutar ne idan tsaftaccen muhalli, kuma mutane na samun tsaftatacen ruwan sha.

Wakiliyar BBC a Lagos Caroline Duffield ta ce ba'a samun kyakkyawan kulawa a asibitoci a Najeriya.