Kisan kare dangi a Kasar Congo

Rwanda
Image caption Kisan kare dangi a Congo

Majalisar dinkin duniya ta yi wani bincike wanda ke nuna irin cin zarafin da aka yiwa 'yan kabilar hutu a lokacin yakin basasar da aka yi a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

BBC ta samu halin ganin daftarin rahoton, wanda ya yi karin haske akan irin cin zarafin da aka yiwa bil adama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Wani abu mai mahimmanci da rahoton ya gano shine, bayanai daki- daki akan takaddamar da aka dade ana yi, game da zargin aikata laifin kisan kare dangi akan kabilun Hutu.

Rahoton ya bayyana cewa Kabilun Hutu dake Rwanda wadanda suka yi gudun hijira zuwa Congo, a sanadiyar kisan kare dangin da 'yan Kabilar Tutsi na Rwanda su ka yi musu, sune wadanda abin ya fi rutsawa da su.

Kuma mafi yawancin su mata ne, da yara, da kuma tsofaffi da wadanda basu da lafiya.