Ma'aikatan lantarki a Najeriya sun janye yajin aiki

Ma'aikatan lantarki a Najeriya sun janye yajin aiki
Image caption Ma'aikatan lantarki a Najeriya sunyi korafin cewa ba a cika musu alkawari

Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta dakatar da yajin aikin da ta kaddamar a jiya kasa da sa'o'i 24 da fara shi.

Hakan ya biyo bayan wata doguwar tataunawar da ma'aikatan suka yi ne da gwamnati.

Watakila a fuskanci jinkiri kafin al'amura su daidata saboda kasancewar sojoji a tasoshin samar da wutar lantarkin:

A yanzu haka dai rahotanni daga cibiyoyin samar da hasken lantarki daban daban na Nijeriya na cewa sojoji sun shige cibiyoyin domin kula da su bayan rahotanni suka ambato wani jami'in gwamnati na cewa ta yiwu ayiwa harkar wutar lantarkin zagon kasa a yayin wannan yajin aikin.

Comrade Joe Ajiero wanda shine babban sakataren kungiyar ma'aikatan lantarki ta Nijeriya ya ce babu damar su tura ma'aikatan su su koma bakin aiki matukar sojojin suna wadannan tasoshi; "Babu damar mu yi aiki suna wurin. Su yi aikin ko su bar mu mu yi. Muna daukan su a matsayin yan mamaya."

Yarjejeniya

Yarjejeniyar dakatar da wannan yajin aikin dai an cimma ta ne bayan doguwar tattaunawa da ta kai har karfe daya na daren jiya tsakanin wakilan gwamnatin Nijeriya da na kungiyar.

"An cimma matsayan cewa yau din nan za'a biya a kalla ma'aikata dubu ashirin kudaden su na alawus yayin da ma'aikatna zasu koma bakin aiki. ragowar su kuma za'a biya su kafin karshen wannan mako." In ji Comrade Ajiero

A 'yan makonnin da suka wuce ne dai gwamnatin Najeriyar ta bayar da umarnin a sakam ma ma'aikatan wasu kudade na alawus din domin shawo kan su kar su je yajin aikin, bayan makwanni hakan bai faru ba dalilin da ya sanya ma'aikatan suka fara yajin aiki a jiya.

Image caption Rashin wutan lantarki yasa masana'antu da dama sun durkushe a Najeriya

Yajin aikin na su, na zuwa ne sa'o'i kafin gwamnatin Najeriyar ta gabatar da wani jadawalin magance babban kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin samar da wutar lantarki ga jama'arta miliyan dari da hamsin.

Duk da kasancewar ta kasar da ta fi kowace samar da man fetur da iskar gas Najeriya bata samar da wuta isasshiya ga jama'a da masana'antun ta.

Hakan ya tilasta rufe kamfanoni da dama da masana'antu a yayin da yawa kuma suka yi kaura zuwa kasashe makwabta.