Majalisar dinkin duniya za ta tattauna kan kasar Congo

Babban sakataren majalisar dinkin duniya,Ban Ki-Moon
Image caption Majalisar dinkin duniya zata tattauna kan fyaden da aka yi a Congo

Jami'an diplomasiyya a majalisar dinkin duniya sun ce kwamitin tsaron majalisar zai yi wani zaman gaggawa a ranar alhamis don tattauna batun fyaden da aka yiwa mata fiye da dari da hamsin a jamhuriyar dimokradiyyar Congo

An yi fyaden ne a wurin da ke da nisan kilomita talatin daga wani sansanin majalisar dinkin duniya.

Jami'an majalisar dinkin duniyar da ke kasar Congo sun ce basu san an yi fyaden ba har sai bayan kwanaki goma da faruwar ta'asar.

Daya daga cikin jami'an Roger Meece ya ce mai yiwuwa tsoron abin kunya da fargaba ne suka sa mutanen kauyen yin shiru, inda ya ce za su dau matakan hana afkuwar hakan a nan gaba.