Sabon Nau'in tsuron Alkama

Masana Ilimin Kimiyya a Birtaniya sun gano wani sabon nau'in kwayar tsuron alkama.

Masanan sun bayyana cewa sabon nau'in kwayar tsuron Alkamar, zai taimakawa manoma wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi, da karancin ruwa, da kuma karuwar bukatar abinci saboda karuwar yawan jama'a.

Daya daga cikin masana kimiyyar, Farfesa Neil Hall na jami'ar Liverpool, yace sakamakon wannan bincike zai taimaka wajen saukaka farashin burodi.

A wani bincike da wakilin BBC ta fuskar kimiyya ya yi, yace, gano wannan kwayar tsuron alkamar zai taimakawa masana kimiyya wajen zabar irin da zai iya jurewa karancin ruwa da kuma tsananin zafi.