Nijar na bukatar kudin shirya zabe.

A jamhuriyar Nijar, 'yan siyasa da ma sauran kungiyoyi na nuna fargaba dangane da gudanar da zabubbuka a kasar, saboda rashin samun taimakon kudade daga kasashen waje, duk kuwa da irin alkawurran da suka yi na taimakawa.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Nijar din ce kawai ta samar da CFA biliyan ukku da rabi, daga cikin biliyan ashirin da taran da ake bukata domin gudanar da zaben.

A watan Janairu mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zabe a Nijar din, bayan juyin mulki da sojoji suka yi a watan Fabrairun bana.