Barazanar sallamar Ma'aikatan kamfanin PHCN

A Nijeriya, Kungiyar Kwadago ta kasa wato NLC ta bayyana cewa za ta yaki duk wani yunkuri na sallamar ma'aikatan kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, wato PHCN.

Tsarin da gwamnatin Najeriya ke shirin yi na yin garambawul ga harkar samar da wutar lantarki a kasar, wanda ya kunshi sayar da akalla kashi hamsin da daya cikin dari na jarin ta dake kamfanin, ya janyo fargabar cewa ma'aikatan kamfanin na iya rasa aiyukansu.

Kungiyar Kwadagon ta ce sam, ba ta fargabar cewa ma'aikata za su rasa aiyukansu a sanadiyyar damka al'amuran kamfanin wutar lantarkin wato PHCN a hannun 'yan kasuwa.

Kungiyar ta kara da cewa ko da kuwa 'yan kasuwa sun karbi ikon kamfanin, akwai dokokin da suka fayyace yanda za'a dauki ma'aikata da kuma sallamarsu, don haka ba zai yiwu a wayi gari a ce an sallami ma'aikatan ba.