ANPP ta ce Cif Ezeoke bai koru ba.

A Najeriya, jam'iyyar adawan ANPP ta yi watsi da matakin da wani bangare na jam'iyyar ya dauka, na sauke shugaban jam'iyyar, Cif Ume Ezeoke, da sauran 'yan majalisarsa daga kan mukamansu.

Jam'iyyar ta ce kuskure ne wasu 'ya'yanta suka yi.

Jiya ne wani bangaren ANPPn ya dauki matakin, a lokacin taron majalisar zartarwar jam'iyyar, saboda a cewarsa, wasu 'yan tsirarru ne kawai ke kada akalar jam'iyyar.

Rikice-rikicen da ANPPn ke fama da su, sun sa da yawa daga cikin kusoshinta sun kama gabansu.