Cutar kwalara ta kashe mutane a Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchin Najeriya sun ce adadin mutanen da suka rasu sanadiyar kamuwa da cutar amai da gudawa ,ya kai saba'in da bakwai.

Kungiyar samar da agaji ta Red Cross a jihar ta ce, duk da cewa an fara samun raguwa a yawan mutanen da ke kamuwa da cutar, amma kuma karancin maganin feshi na Chlorine, da ake fuskanta, zai iya mayar da hannun agogo baya.

Ya zuwa yanzu hukumomin jiharBauchin ba su mayar da martani ba, kan zargin rashin kyaun tsari wajen tunkarar annobar.