Cire ayar doka ta 45 daga kundin mulkin Nijar

Niger
Image caption Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar hadin gwiwar kungiyoyin kare hakin bil'adama da demokaradiya wato RODAD sun kaddamar da wani campaign na neman sa hannun sama da 'yan kasar dubu dari, domin yin kira ga gwamnatin mulkin sojin kasar da ta soke ayar dokar nan mai lamba 45 a cikin kundin tsarin mulki.

Ayar dokar sakin layi na uku dai ta ce, sai mutum me kasa da shekaru saba'in da haihuwa, wanda kuma ke da ilmin mai zurfi na akalla matakin digiri na farko ne kadai zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasar.

Kungiyar ta RODAD na ganin wannan doka ta sabawa tsarin demokaradiya.

Tun dai lokacin da kwamitin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar ya fito da wannan dokar, kungiyoyin siyasa da na farar hula su ke ta faman ce-ce-ku-ce a kanta.