Baraka a jam'iyyar adawa ta Najeriya ANPP

Nigeria Assembly
Image caption 'Yan majalisar dokokin Nigeria

'Yan jam'iyyar adawa ta ANPP a majalisar dokokin Najeriya sun bayyana takaicin su dangane da sabuwar barakar shugabanci da ta kunno kai a cikin jam'iyyar.

Hon. Mohammed Ali Ndume shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, ya ce dama can an dade ana samun wannan matsalar, amma sun dauka cewa abin ba zai kai haka ba.

'Yan majalisar sun bayyana cewa sun kafa wani kwamiti da zai yi kokarin sasanta bangarorin dake takaddama a cikin jam'iyyar.

Ranar juma'a ne dai wani bangare na jam'iyyar ta ANPP ya yi wani taro inda ya tsige shugabannin jam'iyyar bisa hujjar cewa wa'adin shugabannin zai kare ba tare da an shirya babban taro na kasa ba don zabar sabbin shugabanni.