Rwanda ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da butulci

Taswirar Rwanda
Image caption Taswirar Rwanda

Gwamnatin Rwanda ta yi gargadin cewa, za ta sake yin nazari game da huldar ta da majalisar dinkin duniya - musamman ta bangaren aikin kiyaye zaman lafiya - idan har majalisar ta sake ta wallafa wani rahoton da aka tsegunta, wanda ke matukar sukar rundunar sojan Rwandan.

Daftarin rahoton - wanda ya shafi shekarun 1993 zuwa 2003 - ya nuna cewa, akwai yiwuwar dakarun gwamnatin Rwanda, 'yan kabilar Tutsi, sun aikata kisan kare dangi a kan Hutawa masu gudun hijira a jamhuriyar demokradiyyar Kongo.

Ministan shari'ar Rwandar ya shaidawa BBC cewa, majalisar dinkin duniya tayi wa kasarsa yankan baya, kuma bai kamata ta wallafa abinda ya kira: rahoto marar kan gado ba.

A yanzu haka dai Rwanda na da dubban sojojin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan, a karkashin rundunar hadin gwiwa ta majalisar dinkin duniya da Tarayyar Afirka.