Bayani kan dalilan soke zaben Abiola

Kudirat Abiola
Image caption Kudirat Abiola, wadda aka kashe a rikicin zaben 12 Yunin 1993

A Nijeriya, yayinda ake ci gaba da shirye shiryen tunkarar zabe a farkon shekara mai zuwa, wani mai fada aji a yankin kudu maso yammacin kasar, kuma jagoran al'ummar Yarbawa Musulmi, Alhaji Aresekola Alao, ya fito ya yi tsokaci game da dalilan soke zaben ranar sha biyu ga watan Yunin 1993.

Alhaji Aresokola ya ce ya yi magana ne a matsayinsa na aboki ga Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriyar, wanda gwamnatinsa ta soke zaben, da kuma Marigayi Cif MKO Abiola, wanda ake cewar shi ne ya lashe zaben.

Wasu dai na kallon fitowa a yi magana game da soke zaben a yanzu, tamkar wani kokari ne na wanke sunan Janar Babangidan, wanda ke son tsayawa takara zaben badi.