Babban bankin Japan ya yi wani taron gaggawa

Japan Central bank governor
Image caption Gwamnan babban bankin Japan

Gwamnan babban bankin Japan Maasaki Shirakawa dai ya dawo birnin Tokyo ne daga Amurka domin yin wani taron gaggawa.

Karuwar darajar kudin kasar ta Japan wato Yen shine ke taso da matukar damuwa.

Wannan dai na dakile kaifin gasa a matakin fitar da kaya zuwa wadansu kasashen domin sayarwa, sannan kuma ya sa yanayin tattalin arzikin kasar tafiya a hankali.

A makon da ya gabata ne dai shugaban kamfanin kirar motoci na Suzuki yayi kira ga gwamnati kan cewa ya kamata ta saurari kokensu.

Tuni dai aka rage kudin ruwan kasar.

Yanzu kuma babban bankin kasar ya yanke shawarar tsunduma miliyoyin kudade a cikin kasuwannin kudi na kasar, da zummar samarwa bankuna bashi mai rangwamen kudin ruwa.

Fatan dai shine domin su kuma su taimakawa 'yan kasuwa da ranchen kudade, wanda zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai wadansu a kasar na da shakku game da yiwuwar haka, musamman ma da farashin kayan masarufi ya yi kasa, wanda hakan ke nufin karin kudin ruwa.

Sai dai kuma wannan yunkurin na babban bankin ko babu komai, ya taimaka wajen farfado da darajar hannayen jari a kasar, tare kuma da rage kaifin darajar kudin Yen din.