Wata badakala ta taso a wasan kurket

Ingila ta lashe wasan kurket din da ta buga da Pakistan a nan London, a daidai lokacin da ake ta zargin cewa an shirya almundahana.

Hukumar kula da wasannin kurkit ta duniya ce ta yanke shawarar a cigaba da wasan, duk kuwa da cewa an kama wani mutum, dangane da shirin yin zambar, wanda ake zargin ya shafi wasu 'yan wasan kurkit din Pakistan:

Wakilin BBC ya ce, a yanzu hukumomin wasan kurket na Pakistan da Ingila, suna taimakawa 'yan sanda a binciken da suke gudanarwa.

Manajan 'yan wasan kurket na Pakistan ya ce zargin almundahanar na da girma kwarai.