Pakistan za ta binciki zargin da aka yiwa 'yan wasanta

'Yan wasan Kruket din Pakistan
Image caption 'Yan wasan Kruket din Pakistan

Pakistan za ta tura wata tawagar kwararrun jami'an Hukumar Gudanar da Binciken kasarta zuwa London, domin duba zarge-zargen da aka yiwa wasu 'yan wasan kurkit na Pakistan din, na aikata zamba da ta shafi caca.

A daidai wannan lokacin kuma, an bada belin mutumen da ake zargi da hannu dumu-dumu a lamarin, watau Mazhar Majeed, wanda ke zaune a London.

An kama shi ne bayan an yi zargin cewa, ya ba wasu 'yan wasan kurkit din Pakistan su biyu wasu kudade, domin su karya ka'idojin wasan da gangan.

Praministan Pakistan din ya ce sun ji kunya sosai, yayin da wasu tsoffin kyaftin biyu, na kungiyar wasan kurkit din kasar - watai Asif Iqbal da Imran Khan - suka ce ya kamata a dauki mataki.

Imran Khan ya ce, idan har zarge-zargen sun tabbata gaskiya, to ya kamata a yi masu hukuncin da zai zama darasi ga na baya.