A yi wa kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi gyaran fuska

Ban Ki-moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Ban Ki-moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Wani rahoto akan takaddamar da ta dabaibaye kwamitin kula da yanayin majalisar dinkin duniya na IPCC, ya ce kwamitin na bukatar gyaran fuska sosai, da kuma kwakwaran shugabanci. Shugaban kwamitin da ya rubuta rahoton ya ce, su na bada shawarar a aiwatar da manyan sauye-sauye a tsarin tafiyar da kwamitin, wadanda su ka yi imanin za su karfafa aikinsa na yau da kullum, da kuma taimakawa wajen yanke shawarwari.

Daga karshe rahoton ya ce, galibi kwamitin na IPCC ya sami nasara a ayyukan da yayi.

An nemi a shirya rahoton ne, bayan da masu suka sun gano wasu kura-kuran da kwamitin na IPCC yayi a cikin takardun da ya rubuta, kamin babban taron kasashe a kan dumamar yanayi, wanda aka yi a Copenhagen.