Amirka ta sa wa Korea ta Arewa sabon takunkumi

Kim Jong Il, shugaban Korea ta Arewa
Image caption Kim Jong Il, shugaban Korea ta Arewa

Amirka ta fadada takunkumin da ta sa wa Korea ta Arewa, wanda ya shafi harkar kudade, domin horonta akan nutsar da jirgin ruwan yakin Korea ta Kudu a watan Maris.

Sabon takunkumin, wanda zai shafi kamfanonin Korea ta Arewan, da kuma akalla mutum guda, ya bada umurnin a ci tarar kamfanonin da ke cinikin makamai, da kayayakin kawa, da fataucin miyagun kwayoyi, da kuma masu yin kudin jabu.

Korea ta Arewan dai ta ce bata da hannu a nutsewar jirgin ruwan Korea ta Kudun, wadda ta haddasa mutuwar sojan ruwa arba'in da shidda.