Iraki na kan hanyar samun yanci kai

Nuri Maliki
Image caption Firayim Ministan Iraki, Nuri Al Maliki

Yayinda Amurka ke janye sojojinta daga filayen daaga a Iraki, Pira ministan Irakin, Nuri-Al Maliki ya bayyana wadanda ke cewa kasarsa ba za ta iya kasancewa ba tare da taimakon sojojin Amirka ba, da cewa makiyan kasar Iraki ne.

A wani jawabi da ya yi ta talabijin, Mr Al Maliki ya ce Iraki na kan hanyar sake samun 'yancin kanta, kuma ya dage kan cewa sojoji da 'yan sandan Irakin suna da karfin tabbatar da tsaron kasar.

Har yanzu dai akwai sojojin Amurka dubu 50 da za su ci gaba da zama a Iraki a matsayin masu bada shawara, kuma a Amirka ta amince ta janye su a karshen shekara mai zuwa.

Mista Al-malika ya yi amanna cewa an kitsa wani makirci ne don hana Amurkawa ficewa daga kasar ta Iraki.

Kuma ya bayyana masu yin hakan a matsayin makiyan kasar.

A wani jawabi da yayi ga 'yan kasar ta talabiji, Nuri Al-maliki ya ce tun bayan da aka bada sanarwar janye sojojin Amurka daga kasar,kasar ta sa ta maido da 'yancinta.

Ya ce dakaru da kuma 'yan sandan kasar na iya daukar dawainiyar tsaronta,sa'annan kuma zasu samu taimako daga ragowar sojojin Amurka guda dubu hamsin da suka rage a kasar.

Ya ce; "A yau, Iraki kasa ce mai 'yanci,kuma ita ce ke da nauyin dukkanin abubuwan da suka shafe ta.

Ranar talatin da daya ga watan Agusta zata kasance ranar da 'yan kasar ta Iraki ba zasu manta da ita ba domin kuwa zasu kasance masu alfahari.

"Daga yau,sojojinmu,da kuma sauran jami'an tsaro za su ci gaba da tabbatar da tsaron kasar,da kuma kare ta daga duk wani farmaki daga ciki ko wajen kasar." In ji Al Maliki